Muna Shan Wahala Sosai Wajen Samun Mazajen Aure – Rashida Abdullahi

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan wasan Hausa na Kannywood kuma yar siyasa wato Rashida Adamu mai sa’a ta bayyana cewa suna matukar shan wahala yanzu wajen samun mazajen aure.

Jarumar dai ta bayyana hakan ne a yan kwanakin nan kamar yadda Mujallar fim ta ruwaito, ta bayyana cewa a duk lokacin da ta samu mijin aure, to fa a shirye take da ta tare zuwa dakin mijinta.
Jarumar ta kara da cewa: “Samun Mazan Ne Da Wahala, Amma Ko Yanzu Na Samu Miji Da Gudu Za Tayi Aure”.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa jarumar tuni ta dauke kafar ta daga fitowa a matsayin jaruma a cikin fina-finan Hausa na Kannywood sannan kuma ta tsunduma cikin harkokin siyasa inda daga baya ma har ta samu mukamin mai bayar da shawara ga Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Post a Comment