Jarumar nan ta masana’antar Kannywood wadda take fitowa a matsayin uwa a fina-finai da dama watau Hadizan Saima ta bayyana dalilin ta da ya sa yanzu bata marmarin sake yin aure kwata-kwata a halin yanzu.
Jarumar wadda a halin yanzu tauraruwar ta ke matukar haskawa a farfajiyar masana’antar ta bayyana cewa ita yanzu sai dai ta yi wa mutane bayanin menene aure don kuwa shekarar ta sama da ashirin a gidan miji kafin auren na ta ya mutu.
Jarumar ta bayyana cewa ita tana mamakin yadda mutane suke ta yi mata tsegumi a kan wai ta sake yin aure inda ita kuma a ko da yaushe take shaida masu cewa ai ita tafi kowa sanin aure da kuma muhimmancin sa don kuwa ta jima a cikin rigar sa.
Ta bayyana cewa ita yanzu abinda ya rage mata shine tayi auren yayanta wanda suma sun girma,
Ana tsammanin itama tanajin tsoron aure ne a yanzu ganin abinda ya samu Asma'u Sani, wadda ita ma ta auri wani mutum wanda yayi tsammanin tana da kudi, da ya ga ba haka bane kuma ya cigaba da wulakanta ta.
Zaku iya tambaya a comment mu kuma zamu baku amsa.